Sanin dadin Ilimi abune Wanda sai mai shine yake iya fahimtar dadin shi, Don haka muyi kokari mu samu ilimi mai zurfi, musamman ilimi Alqur'ani da sauran fannoni.
Yana daga garabasar Alqur'ani da baiwar da Allah Madaukakin Sarki yayi wa mai karantashi Annabi Sallallahu Alaihi Wa Sallama ya taba karanta inda kake karantawa (Alqur'ani).
Alqur'anin nan dai a harshen Annabi Sallallahu Alaihi Wa Sallama yace:
خيركم من تعلم القران وعلمه ه
"Mafi alherinku Wanda ya san Alqur'ani kuma ya sanar dashi".
Imamu Ahmad bin Habal Yana cewa:
Idan Kana neman Masoya Allah to makaranta Alqur'ani sune masoya Allah ne.
Alqur'anin shine mai cetone ga makarantansa ranar alqiyama.
Idan abubuwa suka cude, rayuwa tayi kunci, zuciya ta harzuqa, komai ya lalace, to Inna shawartarka da ka lazimce Alqur'ani, zaka sha mamaki.
Comments
Post a Comment