TAKAITACCEN LOKACI NE DAKE!!!
Yawan samari, tare da yawan manema aure, yana rudar yan mata a daidai lokacin da suke kan ganiyar kuruciyarsu, har takai ga idonsu ya rufe, sun kasa banbance tsakanin daidai da kuma rashin daidai, su kasa fahimtar abinda ya dace dasu tare da wanda bai dace dasu ba.
A lokacin da mace ta fara zama mace, tun daga shekaru 13 har zuwa 20, a wannan lokaci shine mace take kan ganiyar kuruciyarta, duk wani kyawun halittarta da cikar haibarta, har ma da duk wasu siffofi masu daukar hankalin maza, a daidai wannan lokacin ne suke bayyana a tattare da ita, wannan yasa mace take samun masoya a wannan lokaci fiye da kowanne lokaci,
Da zarar takai shekara 20 zuwa 25 shima zaka sameta da masoya, amman basukai na baya ba, haka abin zayyi ta tafiya har zuwa lokacin da baifi ka sameta da masoyi guda dayaba, idan akaci gaba da tafiya a haka za'a kai lokacin da koda mutum daya bai zama lallai ka samu a wurin ta ba,
Dukkan macen da ta wadata da lafiyayyen tunani, tanayin amfani da damarta ne tun a lokacin da take tashen kuruciya, ta zabi nagartacce a cikin managartan da suke neman aurenta, marar wayo kuwa sai tayi tunanin wannan masoyan zasu dawwama ne a gareta, sai tayi wasa da damarta, har zuwa lokacin da zata zo tayi da na sanin wasa da damarta da tayi.
Bana mantawa akwai wata daliba da mukayi Islamiyya da ita shekarun baya, ajin mu daya da ita, Allah yayi mata farin jini fiye da duk wata daliba, tana da tarin masoya, cikin masoyanta akwai samari, akwai kuma masu aure, har a cikin malaman mu na wannan makaranta akwai masu sonta, hakanan muma daliban da bamu isa aure ba a wannan lokaci, tana matukar burgemu. 🙈 Allah bai rageta da komai ba, domin ta amsa sunanta mace, bana tunanin zaka kalleta sau daya ka dauke kanka ba tare da ka sake kallonta ba. (Inji mai rubutu)
Amman tayi wasa da damarta, tace ita sam batasan wani abu wai shi aure ba, ita sai tayi kaza da kaza sannan zatayi aure, sauran yan uwanta duk sukayi aure, amman ita taci gaba da karatu.
Maganar da nake yanzu haka, tayi karatun daidai gwargwado, domin ta kammala degree dinta, saidai tana zaune a gida babu aiki kuma babu auren, a gabar da take yanzu babu abinda take so kamar ganin tayi aure, domin dukkan kawayenta daga masu yaya 3 sai masu yaya 4,
A cikin masoyan da suke ta bibiyarta a baya, yanzu babu ko mutum daya, duk sun hakura da ita, satin da ya wuce muka hadu da ita, cikin wasa nake cewa da ita: Akwai wani dan Uwana da ya dan manyanta bayyi aure ba, to yanzu kuma yana son zayyi auren, saboda har ya fara neman matar aure, nake cewa da ita zan turoshi wurinta domin ya ganta, wallahi budar bakinta cewa tayi dani na turo shi, nayi mamakin furucinta kwarai da gaske.
To kamar haka damar take ga kowacce mace,
Kici ribar kuruciyarki ta hanyar zaben nagartaccen mijin da aka yarda da nagartarsa a lokacin da kike da tarin samari, idan kika bari damar tu kubuce miki cike gurbin yana da matukar wahala.
Mun sani aure lokaci ne dashi, amman kuma komai yana tafiya ne bisa silar faruwar wani abu, ba zaki kai kanki ga halaka ba sannan kice ai daga Allah take.
ALLAH YASA MU DACE.
Comments
Post a Comment