Idan Ke Mace ne, Toh Ki Karanta Wannan Saqon Akan Aure👇👇👇.
1. Shi aure ibada ne, duk abinda aka ƙira shi da ibada dole akwai wahala cikin yin sa, dole sai an daure sai an cije an kuma yi hakuri.
2. Aure yana tattare da jarrabawa, wanda mutuwa ce kawai ke iya ganin karshen wannan jarabawar, dole a jarabce ku cikin lamuran ku, kamar yadda Allah yace.
3. Kiyi hakuri da mijin da Allah ya haÉ—aki da shi, matukar zai iya ciyar dake, shayar dake da kuma sauke hakkin kwanciyar aure dan wanna sune ginshikin bayan aure.
4. Indai mutum biyu zasu yi rayuwa, toh ya zama dole ɗaya ya kwari ɗaya, dole wani ya ɓoye wayon sa dan a zauna lafiya ba dan anfi shi wayon ba.
5. Babu wani abinda zai tabbata, musamman zaluncin É—aya daga cikin ma'aurata dole wataran Allah yayi al'amarin sa, indai anyi hakuri toh za a ga karshen komai.
6. Ki sauƙe hakkin da yake akan ki, matsayin na mace Koh matar aure, kar ki yadda dan ba a sauke miki naki ba kema, ki ƙi sauke wa, kowa ƙabarin sa daban.
7. Aure cike yake da matsalolin da Allah kadai yasan iyakar su, ana daura miki aure yau, ki sanya a ranki kina iya shiga matsala ta har abada a kan sa.
8. Ba matar da ba ta fama da wata matsala a gidan miji, cikin 100, 5 ne kawai za a same su da sauki amma sauran ko wacce da nata kalar, kar ki dauka ke kadai ce kike fama.
8. Allah ya rantse sai ya jarabce mu, kuma kowa da kalar ta sa jarabawar, dan haka ki dauki matsalar gidan miji a matsayin kaddarar ki.
9. Babu abinda ke zaunar da aure lafiya, kamar hakuri da kuma juriya, muddun kika lazumci wannan toh Insha-Allah wataran sai labari.
10. Idan har Allah ya albarka ce ku da samun Haihuwa, nan ne zaki nin ka juriyar ki, watarana yaran nan da kika haifah zasu ƙwatar miki da ƴan cin ki.
11. Ki riƙe sana'ar ki sa kyau, Idan kina yi, idan bakya yi, ki samu wanda tayi dai-dai da inda kike ki yi. Kar ki zauna ba sana'a.
Mu hadu a maudu'in mu na gaba
Comments
Post a Comment